On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnan Jihar Ondo Ya Tafi Neman Magani

Gwamnan Ondo Rotimi

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya fara hutun kwanaki 21 domin duba lafiyarsa a kasashen waje, inda ya mika ragamar tafiyar da jihar a hannun mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

A wasikar  da ya aikewa  zauren majalisar dokokin jihar da  ita,  Gwamna  Akeredolu,  Ya ce  mataimaki nasa  zai kasance a matsayin mukaddashin gwamna, har zuwa  lokacin da hutun da  ya  dauka  na neman lafiya zai kare.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Olamide Oladiji  wanda  ya karfi kwafin wasikar,  Ya  ce  gwamnan zai koma bakin aiki a ranar 6 ga watan  gobe.

Ana rika sukar gwamnan sakamakon rashin  ganinsa wajen  gudanar da aiyukan gwamnati, saboda wata rashin lafiya  da yake fama da ita da ba’a baiyana ba, Sai dai hadimansa  sun baiyana cewar  gwamnan  yana cikin koshin lafiya, kafin daga bisani  gwamnan ya aikewa majalisar da wannan wasika.