On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnan Jihar Sokoto Ya Fara Rufe 'Kofa Ga Ma'aikata Dake Zuwa Aiki A Makare

Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto a ranar Alhamis ya fara kulle kofar gidan gwamnati ga ma’aikatan da ke zuwa aiki  a makare.

An ce gwamnan ya tuka kansa a mota zuwa gidan gwamnati  da karfe 8:30 na safe sai dai ya gano cewa yawancin ma’aikatan ba sa ofisoshi daban-daban.

Sai dai ya gamu da masu shara da goge-goge da ma’aikacin jinya daya a asibitin gidan gwamnati, amma ya umarci jami’an tsaro da su kulle kofar kuma kada su bari kowa ya shiga.

Bayanai sunce kofar ta kasance a rufe har zuwa karfe 1 na rana, yayin da manyan ma’aikata da dama ciki har da wasu daga cikin hadiman gwamnan suka gaza samun damar shiga.