On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnan Kano Abba Ya Fara Nadin Mukamai

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da nadin mukaman farko a gwamnatinsa.

Ta cikin wata sanarwa da Sunusi  Bature Dawakin Tofa ya fitar, mukaman sun hadar da  Hon. Shehu Wada Sagagi, shugaban Ma’aikata na fadar gwamnati.

Sai  Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jiha  da Dr. Farouq Kurawa  sakatare na musamman  da Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo amatsayin Chief Protocol da kuma Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren Yada Labarai.


Wadannan nade-nade sun fara aiki ne daga yau Litinin 29 ga Mayu, 2023. 

Sanarwar ta ce an zabi wadanda aka nada ne bisa la’akari da chancanyarsu da  sadaukarwa da kuma aminci.