On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Rabon Kayan Tallafi

ABBA GIDA GIDA

Gwamnatin jihar Kano ta fara rabon kayan tallafi da kuma kayan amfanin gona ga masu karamin karfi da mata da kuma manoma da suka fito daga fadin kananan hukumomin jihar kano 44.

Gwamna  Abba Kabir  Yusuf ne ya jagoranci kaddamar da rabon kayan tallafin a Hukumar bunkasa aikin gona ta jihar kano, KNARDA da ke karamar hukumar Nasarawa  a jiya.

Kayayyakin da za’a raba sun hada da Buhu dubu 297 na Shinkada sai  Buhu Dubu Goma na Masara Da Takin zamani Buhu Dubu 2 da 500  da  Injinan Feshi da sauran kayan amfanin gonad a kuma Awaki da Tumaki da Raguna  har guda dubu 2 da 600.

Gwamna Abba Kabir Yusuf y ace masu bukata ta musamman  suma zasu  ci gajiyar tallafin , sannan kuma ya yi gargadin  cewar duk wani jami’in gwamnati  da aka samu da karkatar da tallafin  zai ‘dandana kudarsa