On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnan Kano Ya Musanta Cewar Ana Shirin Rushe Sabbin Masarautun Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya ce har kawo wannan lokaci babu wani mataki da gwamnatinsa take shirin dauka akan sabbin masarautun jihar Kano,kamar yadda labarai ke karade shafukan sada zumunta, dake baiyana cewar gwamnati na shirin yiwa dokar masarautun gyaran fuska.

Jita jitar ta nuna cewar  Gwamnan Kano na shirin aikewa da wani kudirin doka  gaban zauren majalisar dokokin jihar kano, domin yiwa  dokar masarautun kano kwaskwarima, wanda hakan zai bada damar rushe masarautar Bichi da Gaya da Rano da kuma masarautar Karaye.

Sai dai wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature  ya  fitar a daren jiya, Babu wani labari mai kama da wannan, Kazalika ta  baiyana cewar  dukkanin wasu abubuwa da zasu gudana tsakanin bangaren zartawa  da majalisa, za’a yi su ne a bude domin kowa  ya sani.

Bugu da kari sanarwar  ta tabbatar da cewar,  gwamnan na Kano zai tura da sunayen  mutanen da ake son nadawa kan matsayin kwamishinoni  gaban zauren majalisar dokokin jihar Kano, a makon gobe domin tantancewa.