On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnan Kano Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tara Haraji

DAMBO

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ta amince da nada Alhaji Sani Abdulkadir Dambo a matsayin shugaban hukumar Haraji ta jihar kano.

Dambo wanda  ya kasance  tsohon shugaban hukumar,  a yanzu haka  ya kasance babban mai kididdiga  kan tattara  haraji  a hukumar  tara kudaden shiga ta kasa dake Abuja.

Ya yi digirinsa na farko a bangaren Akantaci a jami’ar  Bayero  dake nan Kano  sannan kuma  yana  da  digiri  na biyu  a bangarorin  Tafiyar da harkokin kudi da Akantanci sannan kuma da bangaren gudanar da harkokin kasuwanci.

Sanarwar  ta baiyana cewar  Dambo yana cikin  mambobin cibiyar  tattara  haraji  ta kasa  sannan kuma yana da gogewa ta tsawon  shekara 20.