On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnan Taraba Ya Musanta Sayen Motocin Alfarma Na Bilyan 2

Gwamna Darius Ishaku

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya musanta rahotonnin da ke cewa majalisar zartawar jihar ta amince masa da fitar da naira milyan dubu biyu domin saya masa motocin alfarma shi da mataimakinsa da kuma matansu

Mai  baiwa  gwamnan  shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Bala Dan-Abu, Ta cikinwata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce rahoton ba bu kanshin gaskiya a cikinsa.

Ya bayyana rahoton dake  cewa majalisar zartaswar jihar ta amince da kudin a matsayin yunkuri  na bata  sunan  gwamnan jihar.

Sai dai jam'iyyar Hamaiyyar  ta  APP  a jihar ta bayyana, amincewa da  sayaen  motocin alfarma da ake zargin sun kai na naira milyan dubu biyu  a matsayin abun ban takaici,  a daidai lokacin da ake  bin  gwamnatin jihar  kudaden fansho da na gratiuty.