On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnan Zamfara Ya Bukaci Buhari Ya Hana Emifiele Tafiya Kasashen Waje

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kada ya bada izinin tafiya hutun karo karatu ga duk wani babban jami’in gwamnati da zai iya kawo cikas wajen rantsar da Bola Tinubu Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Gwamnan ya bada misali da  gwamnan babban bankin Kasa, Godwin Emefiele, wanda ake  rade-radin cewar  ya nemi izinin tafiya  hutun karo karatu daga wajen shugaban kasar, Inda  ya bukaci a hana shi.

Matawalle ya yabawa shugaban kasa da uwargidansa kan kokarin ganin an samu sauyi ba tare da wata matsala ba tare da mikawa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu mulki cikin salama,  sai dai ya koka da yadda wasu jami’an gwamnati ke yiwa  shirin zagon  kasa.

Gwamnan na zamfara ya zargi gwamnan babban bankin kasa,  da aikata lefukan kudi daban daban a kasar nan.

Ya jaddada  cewar  dole ne  gwamnan  na CBN ya tsaya gida Najeriya  domin yin  bayanin duk abin da ya faru a karkashinsa ga gwamnati mai jiran gado.