On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatim Jihar Legas Ta Hana Yin Gine-Gine A Yankin Banana Island Sabod Ruguzowar Wani Bene

BANANA ISLAND

Gwamnatin jihar Legas ta bada umarnin dakatar da dukkanin wasu gine-gine da ake gudanarwa a yankin Banana Island dake birnin na Ikko,Biyo bayan ruguzowar wani bene mai hawa bakwai da ake kan ginawa da aka samu a ranar Larabar data gabata.

Kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso ne  ya baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar, Ya baiyana cewar  an dauki matakin ne,  domin tabbatar da jami’an hukumar   tsara gine-gine  sun gudanar da zuzzurfan bincike a  yankin.

Ya kara da cewar  matakin zai baiwa  gwamnati damar sanin yawan gine-gine  da aka yi a yankin batare da samun amincewar  gwamnati  ba , da kuma zakulo  wadanda aka  gina su bisa amincewar  hukuma.