On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Abia Ta Bankado Likitoci Masu Karbar Albashin Jihar Daga Kasashen Ketare Bayan Ajiye Aiki

Gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti, ya ce an bankado wasu likitoci a cikin tsarin Albashin jihar da suka ajiye aiki suka yi hijira zuwa kasashen waje na ci gaba da karbar albashi daga asusun jihar.

A cewar gwamnan, irin wadannan likitocin na ci gaba da karbar albashi daga jihar duk da cewa sun bar aikin jihar yanzu haka suna aiki a kasashen waje.

Otti ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a taron majalisar kula da lafiya ta jihar Abia na farko a cibiyar taron kasa da kasa, Umuahia.

Gwamnan, yayin da yake nunar da cewa ficewar likitocin ta yi illa ga fannin kiwon lafiyar jihar, ya yi alkawarin magance al'amarin ta hanyar baiwa likitocin tallafin jin kai na musamman daga shekara mai zuwa.