On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Buhari Ta Kwato Dala Billiyan 1 Da Aka Sace Daga Shekarar 2015 zuwa 2022 - Malami

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tace tayi nasarar kwato dala biliyan daya da aka sace tun lokacin da aka kafa gwamnatin a watan Mayu na shekarar 2015.

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami shine ya tabbatar da hakan a ranar Laraba bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a Abuja.

Sai dai Malami yace an zuba kudiyar da aka kwato zuwa sassa daban-daban na tattalin arzikin musamman domin magance matsalar fatara.

A cewarsa, matakin ya yi tasiri sosai kan matakan yaki da  talauci da kuma kawar da matsalolin tattalin arzikin kasa.

Haka kuma Malami bayyana takaici a madadin  gwamnati kan cushe da ake samu a  kasafin ƙudin Najeriya, ya ce akwai damuwa a tattare da hakan, sai dao za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki da zasu magance matsalar.