On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Rahoton Yin Garkuwa Da 'Daliban Makaranta

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewa dalibai takwas ne kawai aka sace tare da wasu mutane inda ta jaddada cewa ba a sace daliban a harabar makarantarsu ba.

Idan za’a iya tunawa a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 10 a makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Awon, karamar hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Sace daliban  dai shi ne hari na baya bayan nan da wasu ‘yan bindiga suka kaddamar  a jihar duk da kokarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ke yi na dakile ayyukan su.

Sai dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce sun samu cikakken rahoto daga hukumomin tsaro kan al’amarin kuma daliban na kan hanyar komawa gida  daga makaranta lokacin da aka sace su.