On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bukaci Jama'a Su Shiga Tsarin Temakekeniyar Lafiya

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta yi kira ga al’ummar jihar nan da su shiga cikin tsarin kula da temakekeniyar lafiya da aka samar domin saukaka hanyoyin samun lafiya cikin sauki batare da wata wahala ba.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano,  Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya yi wannan roko a lokacin da yake zantawa da  manema Labarai, a wani bangare na kula da tsarin lafiya na bai daya na shekarar bana, wanda aka yiwa take  da samar Kyakkyawar makoma ta fannin Lafiya  ga  kowa.

Daga nan sai ya bukaci jama’a da su yi amfani da damar da aka samu wajen cin gajiyar shirin a asibitocin da aka kebe domin inganta lafiyar jikinsu.