On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Jihar Legas ta Rushe Gine-gine Sama Da 100 Cikin Wata 8

Sama da gine-gine 100 ne hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas ta rushe a cikin watanni 8 da suka gabata, a wani mataki na dakile rugujewar gine-gine a jihar.

Alkaluman da aka tattara daga shafin yanar gizo na  hukumar kula da gine-ginen ta Legas sun nuna cewa gine-ginen da aka rushe  ruguje a cikin tsukun lokacin sun hada da wadanda suka tsufa da gine-ginen da ba su da Inganci da wasu haramtattun gine-gine da kuma gidaje.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, a cikin watanni biyun da suka gabata gwamnatin jihar ta rusa akalla gine-gine 23 da ake ganin ba za a iya cigaba da wanzuwa ba ko kuma za su iya haifar da hadari ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Da ya ke mayar da martani game da rushe-rushen  da gwamnatin jihar Legas ta yi a baya-bayan nan, Wani kwararre kan gine-gine, Chukwurah Godfrey, ya ce matakin ya zama dole domin ceton rayuka da dukiyoyi.