On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Jihar Yobe Ta Bada Umarnin Kwashe Mazauna Garurun Dake Cikin Hatsarin Ambaliyar Ruwa

Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin kwashe mutanen garin Usur da Gasma da ambaliyar ruwa ke yiwa barazana a kananan hukumomin Bade da Karasuwa.

Mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idi Gubana shine ya bayar da wannan umarni ranar Lahadi a Gashua lokacin da ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin.

Ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar SEMA da ta kwashe mazauna garuruwan  Usur da Gasma zuwa gidajen da aka gina a JajiMaji.

Mataimakin gwamnan ya ce sun kai ziyarar ne domin jajantawa wadanda bala’in ya rutsa da su da kuma tantance irin tasirin ambaliyar da aka yi domin samun tallafin da ya dace.