On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Kano a Haramta Hada-Hadar Filaye a Jikin Makarantu, Asibitoci

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyar ta na kare kadarorin gwamnati tare da dawo da daidaito a harkokin filaye, inda ta sanar da kwato duk wasu filayen gwamnati da aka ware wa makarantu, asibitoci da sauran cibiyoyin gwamnati a fadin jihar.

Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Birane, Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar duba Makarantar Sakandire ta Mata ta WTC bayan rahotannin mamaye filin makarantar ba bisa ka'ida ba.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa an riga an raba kusan fili 100 a harabar makarantar domin gina gidajen zama, lamarin da ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunta ba.

A ziyarar, Kwamishinan ya kasance tare da Shugaban Kwamitin Musamman na Yaki da Gine-ginen Ba Bisa Ka'ida ba da kuma Darakta Janar na KANGIS, Dakta Dalhatu Aliyu Sani, wanda ya bukaci al'ummar Kano su ba gwamnati cikakken hadin kai wajen gyaran da take yi a tsarin kula da filaye a jihar. Saka sautin DG KANGIS ENG...

Shugabar makarantar, Uwani Ahmad Balarabe, ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan bisa saurin daukar mataki, tana mai cewa mamayar filin makarantar ta yi matukar barazana ga cigaban ta, tare da nuna kwarin gwiwar cewa gwamnati za ta dawo da dukkan filin makarantar tare da kare gadonta na ilimi ga al'ummomi masu zuwa.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Heavy rain shower

    High: 33°C | Low: 23°C