On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Kano ta Bukaci 'Yan Kasuwa su Zuba Jarin a Bangaren Tsaftar Muhalli

Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta yi kira ga masu zuba jari daga yan kasuwa da su saka hannun jari a fannin tsaftar muhalli.

Rahoto: Bashir Farouk Durumin Iya

Gwamnatin ta ce matakin zai inganta lafiyar al'umma, samar da ayyukan yi da kuma gina tattalin arzikin da ya ta'allaka kan tsaftar muhalli.

Kwamishinan Ma'aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron kaddamar da shirin yunkurin yan kasuwa da masu zaman kansu don tunkarar matsalar tsaftar muhalli.

Taron ya haɗa mahalarta daga jihohin Gombe, Filato, Katsina, Kaduna da Sakkwato, tare da wakilan Ma'aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli ta Tarayya, abokan hulɗar cigaba, cibiyoyin kuɗi da kamfanonin da ke aiki a fannin tsaftar muhalli.

Dakta Hashim ya ce Jihar Kano na sake fasalta fannin tsaftar muhalli a matsayin muhimmin ginshiƙi na kare lafiyar jama'a da kuma wata babbar dama ta bunƙasa tattalin arziki.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Heavy rain shower

    High: 33°C | Low: 23°C