Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin sake sabunta tsarin birnin Kano wanda ya shafe fiye da shekaru 30 ba tare da an yi masa cikakkiyar bibiya ba, tare da rufe gine-gine sama da 200 da aka gina ba bisa ka'ida ba cikin wata guda.
Darakta janar na hukumar tsara taswirar harkokin kasa ta Jihar Kano (KINGIS) kuma shugaban kwamitin yaki da gine-gine ba bisa ka'ida ba, Dr. Dalhatu Aliyu Sani, ne ya bayyana hakan yayin wani rangadin kwamitin na tabbatar da bin dokokin gine-gine.
Ya ce sake duba Tsarin Birnin ya zama wajibi sakamakon karuwar al'umma da fadada birnin Kano cikin shekaru da dama.
"Master Plan na Kano bai samu cikakkiyar bibiya ta sabuntawa ba tsawon fiye da shekaru 30. Ganin yadda birnin Kano ke ci gaba da fadada, ya zama dole a sabunta shi domin ya dace da bukatun zamani da ka'idojin tsara birane na kasa da kasa," in ji Dr. Dalhatu."
A cewarsa, cikin watan da ya gabata kadai, kwamitin ya rufe gine-gine sama da 200 da aka gina ba tare da izinin hukumomi ba ko kuma a wuraren da doka ta haramta, ciki har da kan hanyoyin wutar lantarki, magudanan ruwa da kuma filayen da aka tanada domin ayyukan bukatu da amfanin jama'a.

Ya ce aikin ya shafi yankuna da dama, ciki har da titin Ahmadu Bello, Hadejia Road, Eastern Bypass, Western Bypass, Gwarzo Road, Maiduguri Road, Nassarawa GRA, Yahaya Gusau Housing Estate da tsohon CBN Quarters.
"Ba za mu lamunci gine-gine ba tare da bin ka'idojin tsara birane ba. Duk mai son gini ya tabbatar ya samu dukkan amincewar da doka ta tanada kafin ya fara aiki," acewarsa"
Dr. Dalhatu ya bukaci mazauna jihar Kano da su ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani gini da ake yi ba bisa ka'ida ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da daukar matakan tabbatar da tsari da kare rayuka da dukiyoyin al'umma tare da tabbatar da ci gaban birnin Kano cikin tsari.
Comments
Add a comment