Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB), Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya ɗauki matakin ladabtarwa kan wasu jami'an lafiya da aka samu da laifin rashin zuwa bakin aiki, tare da yabawa wasu ma'aikata da suka nuna ƙwazo yayin wata ziyarar ba-zata da ya kai wasu cibiyoyin kiwon lafiya a ƙananan hukumomin Gezawa da Kumbotso.
Farfesa Salisu ya jagoranci tawagar gudanarwar hukumar tare da Shugaban Ƙaramar Hukumar Gezawa, Alhaji Mukaddas Bala Jogana, domin duba yadda ake gudanar da ayyuka a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tsalle Model, Gofaro Model da kuma Panshekara Primary Health Centre.
Ziyarar ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin hukumar na tabbatar da ingantaccen aiki, bin ƙa'idoji da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin jihar.
A Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tsalle Model, Babban Daraktan ya nuna damuwa kan yadda ya tarar da ma'aikata da dama ba sa bakin aiki. Nan take ya sauke Shugaban cibiyar daga muƙaminsa tare da mayar da shi ma'aikaci na yau da kullum, yayin da aka naɗa mataimakinsa ya cigaba da jagorantar cibiyar na riƙon ƙwarya.
Haka kuma ya ba da umarnin dakatar da albashin dukkan ma'aikatan da ba su halarci aiki ba har sai kwamitin ladabtarwa na hukumar ya kammala bincike.
A lokacin da tawagar ta isa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Gofaro Model, Farfesa Salisu ya sake sauke Shugaban cibiyar daga muƙaminsa tare da naɗa mataimakinsa a matsayin shugaban riƙo. Ya kuma gargaɗi masu kula da harkokin lafiya na Ƙaramar Hukumar Gezawa cewa ba za a ƙara lamuntar rashin zuwa aiki, sakaci ko gazawar sa ido ba a ƙarƙashin wannan gwamnati.

Ziyarar ta ƙare ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Panshekara da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, inda Babban Daraktan ya duba yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a sassa daban-daban na cibiyar.
A nan ne aka sanar da shi cewa Kwamitin Raya Unguwa (WDC) tare da haɗin gwiwar mahukuntan cibiyar sun samar da na'urar binciken ciki ta ultrasound, domin inganta kula da mata masu juna biyu da kuma lafiyar iyaye mata.
Bisa kyakkyawan tsarin aiki da haɗin kan al'umma da ya gani, Farfesa Salisu ya yaba wa jami'an lafiya na Ƙaramar Hukumar Kumbotso, shugaban cibiyar, Kwamitin Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCC) da kuma Kwamitin Raya Unguwa bisa jajircewarsu wajen inganta ayyukan kiwon lafiya.
Ya sake jaddada aniyar hukumar na gina tsarin kula da lafiya wanda ke da ɗa'a, inganci da kuma mayar da hankali kan buƙatun jama'a. Ya kuma umarci Sashen Gudanarwa na hukumar da ya bai wa mahukuntan Cibiyar Kiwon Lafiya ta Panshekara, PHCC da Kwamitin Raya Unguwa takardar yabo saboda irin gudummawar da suka bayar wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar Kano.
Comments
Add a comment