On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Kano ta Kaddamar da Cibiyar Kula da Masu Amosanin Jini

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da Cibiyar Kula da Masu Cutar Amosanin jini domin samar da cikakkiyar kulawa da magani ga masu fama da ita a fadin jihar.

Gwamnan ya ce cibiyar za ta rika ba da gwaji kyauta, shawarwari, magani, kula da marasa lafiya bayan jinya, ilimantar da su kan yadda za su kula da lafiyarsu, da kuma sauran ayyukan kula da masu cutar Sickle Cell a wuri guda. Saka sautin Gwamna...

Ya tabbatar wa marasa lafiya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da magunguna da sauran tallafin da ake bukata domin inganta lafiyarsu da walwalarsu.

Yayin jawabin nasa gwamnan ya kara da cewa wannan na cikin alkawuran da ya yiwa al'umar jihar Kano lokacin yakin neman zaben sa, la'akari da wahalhalu da marasa lafiya da kuma masu kula da su ke sha sakamakon radadi da marasa lafiyar ke fuskanta duk lokacin da cutar ta tashi.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce mace-macen mata masu juna biyu da masu haihuwa sun ragu matuka a Kano, daga sama da mutum 1,300 a shekarar 2023 zuwa kusan mutum 300 a shekarar 2026.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Heavy rain shower

    High: 33°C | Low: 23°C