On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamiti Domin Sake Bude Makarantun Kwana A Jihar

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa ya kafa kwamitin mutum 5 domin nazarin yadda za’a sake sake bude makarantun kwana da aka rufe.

Kwamishinan ya ce matakin ya zama dole duba da irin muhimmancin da makarantun ke da shi a harkar ilimi a jihar Kano.

Ya yi nuni da cewa, rufe wadannan makarantu da gwamnatin da ta shude tayi,  za a binciki lamarin da nufin gano ainihin dalilin rufe makarantun baya ga batutuwan tsaro da aka ambata.

A wata sanarwa da daraktan wayar da kai a ma’aikatar Aliyu Yusuf ya fitar, ya ruwaito kwamishinan na cewa kwamitin zai kai rahoto ga ma’aikatar kan halin da  makarantun ke ciki a halin yanzu.


A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 33°C | Low: 13°C