On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Kano Ta Rushe Shatale-Talen Kofar Shiga Gidan Gwamnati

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf, Ta rushe shatale-talen kofar shiga gidan gwamnatin kano, da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta gina.

A daren jiya ne aka yi aikin rushe  wajen,  har zuwa wannan lokaci dai,  gwamnati jihar kano bata fitar da wata sanarwa a kan dalilin da  ya sa  ta rushe  shatale-talen da aka kaddamar a lokacin da tsohuwar gwamnati ta yi bukin cikar kano shekara 50 da kafuwa.

Sai dai  idan ba’a manta ba, Gwamnatin Kano na cigaba da rushe  haramtattun gine-gine da aka yi su a filayen gwamnati, a wani bangare na cika alkawarin da  ta dauka a lokacin yakin neman zabe.