On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Kano ta Ware 24 da 25 Ga Yuli Domin Aikin Tsaftar Muhalli

Kwamitin Tsaftar Muhalli na Wata-wata na Jihar Kano ya kammala shirye-shiryen gudanar da aikin tsaftar muhalli na watan Yulin 2026, inda ya ware ranar Juma'a, 24 ga Yuli da kuma Asabar, 25 ga Yuli, 2026 domin gudanar da aikin a fadin jihar.

An cimma wannan matsaya ne a taron kwamitin da aka gudanar a dakin taro na Ma'aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano. An kira taron ne domin duba yadda aka gudanar da ayyukan tsaftar da suka gabata, tantance kalubalen da aka fuskanta da kuma tsara hanyoyin inganta shirin.

Bayan doguwar tattaunawa, kwamitin ya yanke shawarar ware ranar Juma'a, 24 ga Yuli, domin gudanar da tsaftar muhalli a ofisoshin gwamnati, kasuwanni, tashoshin mota, masana'antu da wuraren kasuwanci a fadin jihar.

Haka kuma, an ware ranar Asabar, 25 ga Yuli, domin tsaftar gidaje da unguwanni, inda ake sa ran mazauna jihar za su tsaftace muhallansu tare da zubar da shara a wuraren da gwamnati ta amince da su.

Kwamitin ya jaddada cewa kula da tsaftar muhalli alhakin kowa ne, tare da yin kira ga mazauna jihar, masu kasuwanci, cibiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki da su fito domin taka rawa wajen gudanar da aikin.

Ya ce tsaftar muhalli na daga cikin ingantattun hanyoyin kare lafiyar al'umma, rage barazanar gurbacewar muhalli da kuma samar da al'umma mai tsafta da koshin lafiya.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 34°C | Low: 23°C