Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano (KSBS) ta yi watsi da wani rahoto da ke dauke da alkaluma kan yawan al'ummar jihar da masana'antu da masallatai da coci-coci da kuma adadin yara kanana marasa iyaye da ake zargin suna yawo a kan titunan Kano.
Darakta Janar na hukumar, Dakta Suraj Sulaiman, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce rahoton da aka danganta da wani Garba Adamu kuma wani shafin yanar gizo mai suna The Sultan of Hausa-Land ya wallafa, ba ya dauke da sahihan alkaluman da hukumar ta fitar. Hukumar ta bayyana cewa adadin masana'antun da ke aiki a Jihar Kano, da suka hada da kanana da matsakaita da manyan masana'antu, ya kai 3,632, sabanin adadin 58 da rahoton ya wallafa. Hukumar ta kuma karyata ikirarin cewa Kano na da masallatai 435,389, tana mai cewa alkalumanta na hukuma sun nuna akwai masallatan Juma'a 2,333 kacal. Haka kuma, KSBS ta yi watsi da ikirarin cewa akwai yara kanana marasa iyaye miliyan 3.67 da ke yawo a titunan Kano, inda ta bayyana adadin a matsayin karya, mai cike da karin gishiri kuma ba shi da tushe a sahihan bayanan kididdiga. Hukumar ta bukaci masu yada rahoton da su janye shi tare da bada hakuri, tana mai jaddada cewa ita ce kadai hukuma da ke da ikon fitar da sahihan alkaluman kididdiga na Jihar Kano.
Comments
Add a comment