On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Kano ta Ƙarfafa Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada matsayinta na nuna halin ba sani ba sabo kan yaki da da cin hanci da rashawa a dukkanin hukumomi da ma'aikatun gwamnati, tana mai nanata aniyarta na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a bangaren gudanar da aiyukan gwamnati.

An sake bayyana wannan matsaya ne a wani taron bitar samun  ƙwarewa  da ka shiryawa  sabbin manyan  sakatarori 19 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa a baya-bayan nan domin su yi aiki a hukumomi daban daban.

Da yake jawabi ga mahalarta bitar da ke gudana a Kaduna, Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Comrade Sa'id Yahya, ya ce taron na daga cikin matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa ɗabi'ar gaskiya da dakile ayyukan rashawa a ɓangaren gwamnati.

A cikin saƙon murya da ya  aikowa Arewa Radio ta manhajar WhatsApp, Comrade Sa'id Yahya ya ce hukumar na ci gaba da samun nasara.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 33°C | Low: 23°C