Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna damuwarsa kan yadda direbobi da sauran masu amfani da hanya ke cigaba da karya dokokin hanya, musamman rashin bin umarnin fitilun zirga-zirga a manyan titunan jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ya shafe kusan awa guda yana taimakawa wajen daidaita cunkoson ababen hawa a mahadar Tal'udu tare da wasu manyan jami'an gwamnati yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani taron gwamnati.
Ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta sake fasalin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano, KAROTA, domin mayar da ita cikakkiyar hukuma mai kwarewa wajen tafiyar da harkokin zirga-zirga da tabbatar da tsaron masu amfani da hanya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce za a kara wa KAROTA karfi domin inganta kula da zirga-zirga, tabbatar da bin dokokin hanya da kuma inganta al'adar biyayya ga dokokin zirga-zirga a fadin jihar.
Gwamnan ya ce duk da biliyoyin nairorin da gwamnatin jihar ta kashe wajen sabunta Kano, da suka hada da girke fitilun zirga-zirga na zamani masu amfani da hasken rana, alamomin hanya da fitilun tituna, har yanzu wasu direbobi na ci gaba da karya dokokin hanya tare da yin watsi da fitilun zirga-zirga.
Ya ce wannan dabi'a na jefa rayukan jama'a cikin hadari tare da lalata kokarin gwamnati na gina birni mai tsari.
Comments
Add a comment