On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Kano Zata Gina Gidajen Tsofaffi A Masarautun Jihar 5

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta samar da gidajen kula tsofaffi a daukacin masarautun jihar guda 5,  kamar yadda ta ke da burin samar da kwas na ayyukan jin dawainiyar jama’a  a Jami’ar Yusuf Maitama Sule.

Sakataren zartarwa na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kano SEMA, Dokta Sale Aliyu Jili, shine ya bayyana hakan a yau, yayin wani horo na kwanaki biyu na masu  tallafawa wuraren kula da tsofaffi, da hukumar ta SEMA ta shirya  hadin gwiwa da ma’aikatar jin kai da ci gaban al’umma ta tarayya.

Jili, ya kara da cewa horon zai taimaka wa ma’aikatan wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata kuma bisa ka’ida. 

Da yake zantawa da wakilinmu Kamaluddeen Muhammad, shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule,  Farfesa Muktar Atiku Kurawa, ya ce jami’ar na shirin samar da wani kwas a jama’ar domin karfafa tsarin na kula da tsofaffi a yankin Arewa maso Yamma.