On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Kano Zata Rufe Wasu Kanfanoni 5 Saboda Taurin Bashi.

wata Kotun Kartakwana a karkashin Mai shari’a Malam Ibrahim Gwadabe ta bawa wasu kanfanoni biyar dake aiki a jihar nan wa’adin makwanni biyu dasu gaggauta biyan bashin kudin rijistar da gwamnati ke binsu, ko kuma a kulle su.

Kanfanoni  Sun hada MTN sai Kanfanin Glo da Bankin Titan Trust  sai kuma Bankin Aso Saving da Kanfanin fansho na Veritas da kuma kanfanin Maersk Shipping.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’ar Yada Labarai ta Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba jari ta jihar Kano, Sa’adatu Suleman  wadda  aka aikowa Arewa Radiyo.

Ta baiyana cewa kin biyan bashin ya sabawa  dokokin yin rijistar kasuwanci  na jihar Kano sashi na 8 da 9 na shekarar 2014.