On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Kano Zata Sake Bude Asibitin Yara Na Asiya Bayero Nan Da Mako 2 - Gwamna Abba

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin cewa asibitin yara na Hasiya Bayero zai koma aiki nan da makonni biyu.

Har ila yau, gwamnan ya umarci kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf da ya gaggauta samar da injuna domin ganin an dawo da asibitin matsuguninsa na asali   cikin sauki.

Gwamna Yusuf a lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda ya kai masa ziyarar Sallah ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da aiwatar da tsarin haihuwa kyauta yadda ya kamata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin mai magana da yawun gwamnan, Hisham Habib, ya fitar.

Ya kuma baiwa ‘yan majalisar zatarwa na gwamnatinsa umarnin da su hada kai da shugabannin kananan hukumomi wajen gano manyan kalubale da ake fuskanta inda ya kara da cewa gwamnatinsa tana kokarin ci gaban Kano.