Gwamnatin Jihar Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Umar Farouk, daga dukkan ayyukan hukuma da tafiye-tafiye, sakamakon zargin cin zarafi da wata bakuwar yawon bude ido daga ketare ta yi masa.
Gwamnatin ta kuma sanar da kafa wani babban kwamiti da zai gudanar da bincike kan zargin tare da ba ta shawarwari kan matakin da ya kamata ta dauka.
Matakin da aka sanar a ranar Talata ya biyo bayan ce-ce-ku-ce da zargin ya haifar a tsakanin al'umma, inda lamarin ya ja hankalin jama'a a cikin Najeriya da wajen kasar.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu na jihar, Bala Zango, ya sanya wa hannu, gwamnatin ta ce ta dauki zargin da matukar muhimmanci.
Sanarwar ta ce Gwamna Dikko Radda ne ya bayar da umarnin kafa kwamitin bincike cikin gaggawa domin gudanar da cikakken bincike kan zargin da aka yi wa Sarkin.
A matsayin wani bangare na matakan da aka dauka, gwamnatin ta ce an dakatar da Sarkin daga halartar dukkan ayyukan hukuma da tafiye-tafiye har sai an kammala bincike.
Gwamnatin ta tabbatar wa al'ummar jihar cewa za a yi adalci, tare da bayyana cewa za ta aiwatar da sakamakon binciken kwamitin da shawarwarin da zai gabatar mata.
Ta kuma yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka da oda, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum yayin da kwamitin ke gudanar da aikinsa.
Comments
Add a comment