On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Najeriya Na Iya Kashe Billiyan 29 Wajen Diyya Ga Mutanen Da Harin Sojoji Na Kaduna Ya Hallaka

Gwamnatin Tarayya na iya biyan kusan Naira billiyan 29.21 ga kimanin mutane 127 da harin bam da aka kai a daren Lahadi ya hallaka a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Othman Ngelzarma, ya shaidawa manema labarai cewa a tsarin shari’ar Musulunci, kowanne daga cikin wadanda abin ya shafa diyyarsa takimanin milliyan 230.

Sai dai ya nunar da cewa Najeriya kasa ce da ba ta damu da aiki da tsarin addini ba, don haka bai san ma’auni da gwamnati za ta iya dauka ba don biyan wadanda abin ya shafa, amma a Musulunci, adadin ya kusan Naira milliyan 230 ga kowane mutum.