On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Hutun Bukukuwan Karamar Sallah ; 2023

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin 21 da kuma  24 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan karamar Sallah a bana.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren na ma’aikatar sa, Dr Shuaib Belgore, ya fitar ranar Laraba.

Ya kuma taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan lafiya.

Aregbesola ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u da soyayya da  hakuri da  zaman lafiya da sadaukarwa irin na Annabi Muhammadu S.A.W.