On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Najeriya Ta Tsawaita Lokacin Dawo Da Zirga-Zirgar Jiragen 'Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta hannun ma’aikatar sufuri a kasar ta sanar da tsawaita lokacin da za’a dawo cigaba da aikin layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna.

Ministan Sufuri Mu’azu Sambo shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna ranar Lahadi a wani rangadi da ya kai don duba yanayin shirye-shiryen dawo da sufurin layin dogon  na Abuja zuwa Kaduna kafin a fara aiki.

Sai dai bai bayar da takamaimiyar  ranar da za a ci gaba da aikin ba amma ya nunar da  cewa ba zai wuce mako guda ba.

A cewar ministan, gwamnatin tarayya ta bullo da wani sabon tsarin siyan tikitin jirgin, wanda a cewarsa shi ne mafarin binciken tsaro wanda zai baiwa gwamnati damar tantance wadanda ke hawa jirgin a kowane lokaci.

Idan za a iya tunawa dai a makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa aikin layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna zai dawo a ranar 28 ga watan Nuwamba.

An dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna na wani dan lokaci watanni takwas da suka gabata, lokacin da 'yan ta'adda suka tayar da bam, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mutane tare da yin garkuwa da fasinjoji sama da 60, wadanda bayan tsahon lokaci aka sake su.