On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Najeriya Tace Zuwa Watan Disambar 2022 Zata Kawo Karshen Ayyukan Ta'adanci A Kasar

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci a kasar zuwa watan Disambar wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola shine ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa kan harkokin tsaro a Abuja.

Aregbesola ya ce kokarin da sojoji ke yi a halin yanzu tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro ya sa ‘yan bindiga da dama sun waste  daga  sansanoninsu.

Aregbesola ya ce: “Muna bai wa ’yan Najeriya tabbacin isashen tsaro da aminci, shi ya sa shugaban kasa ya umarce mu da mu sanar da ku cewa daga yanzu zuwa watan Disamba, kullun tsaro da aminci da za ku samu za su inganta.

“Abin da muke fama da shi yanzu ba wani abu ba ne face harin matsorata da aka tarwatsa maboyansu a wurare daban-daban, wanda suna yin haka ne domin a rika ganin cewa har yanzu da sauran karfinsu.

“Babbar manufarmu ita ce kawar da su gaba daya kasa sannan mu dawo da aminci a kowane taki na fadin kasar nan; kuma da izinin Allah hakan zai samu zuwa watan Disamba na wannan shekara.

“Za a ga da kamar wuya amma zai yiwu, domin mun shirya domin tabbatar da aminci da tsaro a kowane taki a fadin kasar Najeriya, kuma tuni aka bayar da umarnin yin hakan,” in ji Aregbesola.

Kalaman Ministan Harkokin Cikin Gidan sun zo ne bayan takwaransa na Ma’aikatar Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce a barazanar tsaro da Najeriya ta fuskanta a ’yan shekarun nan ita ce mafi muni tun bayan yakin basasa.

Lai Mohammed ya ce matsalolin tsaro a kasar sun hada da tayar da kayar baya da yin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da neman ballewa daga kasar da satar mai da fashi da sauransu.

Ya ce, “Tabbas wannan shi ne kalubale mafi girma da zaman lafiya da tsaron kasarmu suka fsukanta tun bayan yakin basasa a 1967 zuwa 1970.”

Sai dai ya ce hakan ya kusa zama tarihi domin matakan da gwamnati ta dauka a kan ’yan ta’adda da dangoginsu sun sa suna neman inda za su tsere.

“Wadannan wasu kalubale ne da ke iya buwayar kowace kasa, amma Alhamdulillahi da irin kokarin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A nasa bangaren, ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ya ce ‘yan sanda sun kara sanya ido akan manyan titunan kasar nan.