On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Najeriya Zata Gana Da Kamfanonin Sufurin Jiragen Sama Na Kasashen Waje

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen  balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da  kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren  da warware matsalar.

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da  Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

Har yanzu zuwa karshen mako  matsalar  tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa'o'i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro.