On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Taraiyya Na Son Shafin Facebook Ya Biya Ta Naira Bilyan 30

FACEBOOK

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bai wa hukumar kula da tallace-tallace ta kasa, izinin yin sammacin kanfanin Meta, wanda shi ne mamallakin katafaren shafin sada zumunta na Facebook.

Kotun ta bayar da umarnin ne a bisa bukatar da  hukumar  ta shigar a gaban kotu na neman kanfanin ya biya ta  Naira biliyan 30   saboda  karya dokokin talla a Najeriya.

Za a tura  sammacin ne  kai tsaye  zuwa  shalkwatar   kamfanin Meta  dake  Amurka wanda ya kasance  mallakin shafukan sada zumunta na facebook da Instagram  da  Messenger da  kuma  WhatsApp.

Hukumar kula da tallace-tallace  ta kasa  ta baiyana cewar  yadda kanfanin ke  wallafa  wasu  tallace – a shafin nasa  a nan       Najeriya ba tare da samun amincewarta ba,  Haramun ne, kuma ya sabawa doka.

Hukumar ta kuma yi ikirarin cewa mafi akasarin tallar da ake sakawa a shafin na Facebook a nan Najeriya  ya  ci karo  da  al'adun  kasa da  tanadin kundin tsarin mulki da kuma tunanin 'yan kasa.