On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Gwamnatin Taraiyya Ta Amince Da Yin Amfani Da Fasahar Alkinta Bayanai A Wuri Daya

PANTAMI

Gwamnatin tarayya ta amince da yin amfani da wani tsarin fasahar alkinta bayanai a wuri daya.

An amince da yin amfani da tsarin ne a   yayin taron  majalisar zartarwa na  kasa da  shugaban kasa  Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, farfesa  Isa Pantami ya ce fasahar  alkinta  bayanai  a wuri  daya  zata  temaka wajen kare bayanan daga masu kutse  a na’ura  ko  kuma  yin wani abu da bai dace  ba.

Pantami ya kara  da  cewa,  majalisar  zartarwar  ta kasa  ta umurci hukumomi da su hada kai da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa domin  tabbatar da  sunyi amfani da tsarin.

Ministan ya bayyana cewa fasahar Alkinta bayanai  a wuri  daya  ta Blockchain  ta  dace da yin aiki  bangarori da yawa   kamar  aikin  banki  da fannin tsaro  da  ilimi da kasuwanci da dai sauransu.