On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Taraiyya Ta Bude Gadar Naija Ta Biyu Domin Saukakawa Matafiya

GADAR NAIJA TA BIYU

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin bude babbar gadar Naija ta biyu , domin cigaba da yin amfani da ita.

Kazalika ya shawarci masu amfani da hanya da su rika tukin cikin nutsuwa akan gadar, kamar yadda  ya baiyana haka yayin bukin bude gadar da aka yi  domin yin amfani da ita na tsawon wata daya, a lokacin da ake bukukuwan karshen shekara.

Da yake jawabi ta bakin ministan aiyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, Shugaban kasar  ya ce  makasudin gina gadar shine domin kare  rayuwa  da kuma rage  fatara da ake fuskanta a sakamakon cunkuson ababen hawa na tsawon  sa’oi da ake samu a tsohuwar gadar  Naija ta farko da ake samu.