On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnatin Taraiyya Ta 'Dauki Hayar Lauyoyin Da Zasu Kare Sanata Ekweremadu

Gwamnatin taraiyya ta karkashin Babban Ofishin Jakadancin Kasar nan dake Burtaniya, Ta dauki hayar wasu lauyoyi da zasu kare tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweramadu tare da Mai Dakinsa Beatrice, a sakamakon zarginsu da yunkurin cire sassa jikin Dan Adam.

Shugaban Majalisar Dattawa  Sanata Ahmad Lawan ne ya baiyana haka, Jim kadan bayan wata ganawar sirri da zauren majalisar yayi a zamansa  na yau Laraba, Sannan kuma ya baiyana cewa a cikin makon nan ne, tawagar Majalisar Dattawa zata ziyarci Ike da Mai Dakinsa wadanda suke a birnin Landan.

 

Kazalika Shugaban Majalisar Dattawan, Ya baiyana cewa matakin da aka dauka  na kamawa tare da tsare sanata Ike Ekweramadu da Mai Dakinsa a birnin Landan, ya sabawa tanade-tanade da ofishin jakadancin kasar nan dake birin Landan ya tsara.

 

Bugu da kari  ya baiyana cewa Majalisar Dattawa, zata tattauna  da  Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar nan tare da Ofishin Jakandacin Najeriya dake Landan  akan kamen da ‘yan sandan birnin landan suka yiwa  sanatan.