On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Gwamnatin Taraiyya Ta Fitar Da Naira Bilyan 19 Domin Horas Da Masu Shirin N-POWER

Gwamnatin taraiyya ta amince da fitar da zunzurutun kudi har naira bilyan 19 da milyan 24 domin aikin horas da masu shirin N-Power Dubu Hamsin, da kuma saka fitulu a cikin filayen jiragen saman Fatakwal da Legas da kuma Abuja.

Kazalika kudin ya kunshi  biyan  kudin aikin tuntuba  na aikin samar da hasken lantarki mai karfin megawa 40 a jihar Gombe,  ga kanfanin  Dadin kowa , da  kuma aikin ‘kawata  shalkwatar  hukumar  sufurin jiragen ruwa  ta kasa  dake  yankin Victoria Islanda a Legas.

Ministan kula da harkokin jin kai da kuma ministan  sufurin jiragen sama na kasa,  tare da ministan albarkatun ruwa  na kasa, sune suka baiyana  haka ga manema labarai,  jim  kadan bayan kammala zaman majalisar zartawa  na gaggawa  da aka yi jiya.

Ministan  kare afkuwar Bala’oi ta kasa, Hajiya Sadiya Faruk ta  ce an fara shirin N-POWER ne  tun daga shekarar 2016.