On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Taraiyya Ta Gana Da Shugabanni Da Iyayen Jami'oin Gwamnatin Taraiyya

BUHARI DA ASUU

A yaune gwamnatin taraiyya ta gana da shugabanni da kuma Iyayen jami’oin gwamnatin taraiyya dake fadin kasar nan, a wani mataki na kokarin kawo karshen yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU Ke kanyi.

A yayin  ganawar, Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu ya baiyana yajin aikin sai baba ta gani da kungiyar ASUU ke kanyi, a matsayin wani abun tozarci da kuma rikitarwa.

Adamu yace akwai bukatar  bangarorin biyu su cimma kwakwkwarar  matsaya kan dukkakin abubuwan da aka cimma yarjejeniya a kansu a shekarar  2009, kasancewar makwanni  biyu da suka gabata sun kasance  mafi muni ga bangaren ilimi a kasar nan.

Ministan Ilimin ya Ambato shugaban kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, wanda ya baiyana cewa a halin yanzu kungiyar ba zata sasanta da gwamnati mai ci akan yajin aikin ba, inda  ya baiyana cewa ya zama wajibi a janye matakin domin  ceto  fannin ilimi a kasar nan.