On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Taraiyya Ta koka Akan Karuwar Masu Ta'amulli Da Miyagun 'Kwayoyi

OSINABAJO VS BUHARI

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yace gwamnatin tarayya ta damu matuka kan yadda ake harkokin sha da fataucin miyagun kwayoyi, tare da ayyukan ta’addanci, a fadin kasar nan.

Osinbajo ya bayyana haka ne yau, a wani bngare na ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da majalisar dinkin duniya ta ware, a fadar mulki ta VILLA dake Abuja.

Osinbajo yace hakika an damu kwarai da gaske kan lamarin, bisa yadda ake samun karuwar masu shiga harkar gida da waje.

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin magance matsalar, ya bukaci malaman addini da iyaye, kan su ja hankalin matasan kasar nan.

A nasa bangaren shugaban hukumar hana shad a fataucin miyagun kwayoyi na kasa Buba Marwa, yace hukumar ta samu nasarori da dama, a wannan lokacin.