On Air Now

Maraicen Asabar

6:00pm - Midnight

Gwamnatin Taraiyya Zata Hukunta Gidajen Man Da suka Ki Yin Amfani Da POS

NNPC

Gwamnatin taraiyya ta fara baza jami’an tsaronta zuwa gidajen mai domin tursasawa masu gidajen man yin amfani da POS ko kuma karbar sakon tura kudi ta banki.

Hukumar  kula  da harkokin albarkatun mai  ta kasa  ita  ce  ta baiwa  gidajen  man   umarnin fara  yin amfani da wannan  tsari  kamar  yadda  yake  kunshe  cikin wata  sanarwa  da aka fitar  jiya  a Abuja.

To sai dai  sakataren  kungiyar  Dillalan mai  ta kasa  masu zaman kansu  reshen  Abuja  da Suleja, Mohammed  Shu’aibu, Ya  ce  suma   matsalar  rashin wadatuwar  kudi a  hannu  tana  shafar  kasuwancinsu,  Yana mai cewar babu  yadda  zasu  yi  wasu  tafiye  tafiye  domin yin huldodinsu  da  suka  saba, dole sai anyi amfani da tsabar  kudi a  hannu.

Kazalika  ya  ce  hanyoyin sadarwar  da ake  amfani dasu wajen hada-hadar kudi  ta  banki  basu  da ingancin da ake  tsammanci , a  saboda  haka  dakon  samun tabbacin  tura  kudin da mai sayen mai  zai  yi a  gidan mai, zai  sai  a samu  cunkuson ababen hawa  a  gidajen man.