On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Taraiyya Zata Kashe Naira Bilyan 24 Wajen Samar Da Hanyoyin Sadarwa A Filayen Jiragen Sama Da Kasuwanni Da Kuma Jami'oi

Farfesa Fantami

Taron Majalisar zartaswa na kasa ya amince da bayar da wasu kwangiloli guda biyu akan kudi naira milyan dubu 24,wanda ya hada da samar da hanyoyin sadarwa na kyauta a wasu wurare guda 75 da jama’a ke amfani dasu,wanda suka hada da Filayen jiragen sama dake fadin kasar nan domin tallafawa kanana da kuma matsaikatan masana’antu.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ne ya  baiyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartawa na kasa  da  shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadarsa  dake  Abuja.

ya ce  wuraren sun hada  da filayen jiragen sama  sai Kasuwanni da manyan makarantu, inda  jama'a zasu rika amfani da  hanyoyin sadarwar  a kyauta.

Ya kara  da cewar  Hukumar  sadarwa  ta kasa  ita  ce  zata  jagoranci gabatar da wani bangare na aikin a  yayin da wani  kason kuma zai kasance  a karkashin  kulawar  ma’aikatar sadarwa da cigaban tattalin arziki na zamani  ta kasa.