On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Taraiyya Zata Maye Gurbin Likitocin Dake Yajin Aiki Da Ma'aikatan Wucin Gadi

LIKITOCI

Gwamnatin taraiyya ta yi barazanar daukar Hayar Likitoci tare da biyansu albashi da hakkokin Likitoci masu neman kwarewa da suka shiga yajin aiki.

Ministan kwadago Chiris Ngige ne  ya  baiyana haka yayin wata hira da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels.

A jiya ne kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa suka fara  yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyar  domin ganin an biya masu bukatunsu.

Ya kuma baiyana cewar  Kungiyar  likitocin ta  nuna rashin girmamawa ga uwar kungiyar lIkitoci  ta kasa, kasancewar  a yanzu haka  gwamnatin taraiyya  tana  tattaunawa  da ita a madadin kungiyar.

A wani bangaren kuma,

Gwamnatin taraiyya  ta ce  a yanzu haka ana tattaunawa  tsakanin masu  ruwa  da tsaki kan yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki biyar , Wanda kungiyar Likitoci masu neman kwarewa  ta kasa  ta fara  a tsakar daren jiya.

Da yake amsa  tambayoyin manema Labarai jiya a Abuja, Daraktan sashin kula da lafiyar al’umma na Ma’aikatar lafiya  ta kasa, Dr Morenike Alex Okoh, Ya  ce  gwamnatin taraiyya  ta damu matuka  da  tafiya yajin aikin.

Likitocin dai na neman a yi masu karin Albashi da kaso 200 cikin 100  daga  abunda ake basu a halin yanzu.

Sai dai ministan Kwadago, Chiris  Ngige  ya  gargadi  Likitocin masu neman kwarewa kan tafiya  yajin aikin da suka yi,  wanda  ya baiyana a matsayin haramtacce.