On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Taraiyya Zata Samu Sama Da Bilyan 124 A Bangaren Tatsar Harajin Kayayyaki

HARAJI

Gwamnatin tarayya za ta samu kimanin naira bilyan 124 da milyan 26 a cikin shekara daya daga bangaren harajin shigo da kayayyaki cikin kasar nan, wanda aka dora bisa kaso sifili da digo 5 bisa 100 kamar yadda yake kunshe a cikin dokar tafiyar da harkokin kudi ta shekarar 2023.

Dokar kudi ta  shekarar  2023 wadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a ranar 28 ga watan Mayun 2023, Ta yi tanadin cirar kaso Sifili  da digoi 5 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya daga kasashen waje.

A cewar dokar, za a dora harajin  kaso Sifili da digo 5 kan kayayyakin da ake shigowa da su Najeriya daga kasashen waje.