On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Taraiyya Zata Yanke Alakar Dake Tsakaninta Da Wasu Kanfanonin Samar Da Lantarki

LANTARKI

Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ta fara katse huldar dake tsakaninta da wasu kamfanonin samar da wutar lantarki a kasar nan , sakamakon rashin bin ka’idojin kasuwancin wutar lantarki da suke yi.

Duk da cewa ba a bayyana sunayen kamfanonin wutar lantarkin da abin ya shafa ba, gwamnatin ta bayyana cewa,  an dora  harkokin tafiyar  da wutar lantarki a kasar  nan, bisa doron ka’idojin samar da hasken lantarki a kasar nan.

A cewar Gwamnatin Tarayya, Dole ne kanfanoni suyi biyayya  ga  dokokin da gwamnati ke  tafiya a kansu.

Shugaban sashin kula da harkokin na kanfanin dakon wutar lantarki na  kasa  Edmund Eje, ya ce   a  halin yanzu  kanfanonin samar da wutar lantarki suna yin watsi da dokokin wanda yin hakan abun takaici ne.