On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Tarayya Ba Zata Iya Ciyo Bashi Domin Biyan Bukatun ASUU Ba - Dave Umahi

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya ciyo bashin Naira tiriliyan 1 da milliyan 1 ba domin biyan bukatun kungiyar ASUU.

Kungiyar ta shafe  fiye da wata biyar tana yajin aiki.

Umahi, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Gabas ya bayyana hakan a ranar Laraba  a lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga asusun tallafawa ‘yan sandan kasarnan  a Abakaliki, babban birnin jihar ta  Ebonyi.

Ya ce bai dace Najeriya ta ciyo bashin kudi sama da naiara trilliyan 1 domin  biyan bukatar ASUU ba, duk da cewa bukatun na gaskiya ne.

Amma ya kara da cewa sannu a hankali za a iya magance bukatun.

Sai dai ya yi kira ga malaman jami’o’in da su nuna yakana da  fahimta domin  kawo karshen yajin aikin.

(Karin Magana: Zara bata barin dami)