Gwamnatin Tarayya ta bukaci 'yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta da su hana 'yan bindiga da 'yan ta'adda samun farfagandar da suke nema, tana mai cewa aikin jarida mai ɗa'a da ƙwarewa na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma yaƙi da tsattsauran ra'ayi.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron farko na Arewa Media Summit da Ofishin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ya shirya a Kano.
Ya ce kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da tsattsauran ra'ayi ta hanyar yaɗa saƙonnin haɗin kai, jajircewa da fata, maimakon ba ƙungiyoyin masu aikata laifuka damar yaɗa manufofinsu.
Ministan ya ƙara da cewa dimokuraɗiyya na bunƙasa ne idan gwamnati ta kasance mai gaskiya da riƙon amana, 'yan ƙasa suka taka rawarsu yadda ya kamata, sannan kafafen yaɗa labarai suka gudanar da aikinsu bisa ƙwarewa, adalci da gaskiya.
Ya kuma bayyana cewa duk da irin sauyin da fasahar zamani ta kawo wajen sadarwa, inda kusan kowace wayar hannu ta zama kafar yaɗa labarai, hakan ya kuma ƙara yawaitar yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ke iya haddasa ruɗani tare da raunana haɗin kan ƙasa da amincewar jama'a.
Tun da farko, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa tattaunawa tsakanin gwamnati, al'umma da kafafen yaɗa labarai ta hanyar tabbatar da riƙon amana, ɗaukar nauyi da kuma sadarwa mai ɗa'a.
Ya ce gwamnati na da alhakin samar da sahihan bayanai cikin lokaci, yayin da al'umma ke da alhakin mu'amala cikin nagarta, kuma kafafen yaɗa labarai su kasance gada tsakanin shugabanni da jama'a ta hanyar sahihan rahotanni masu daidaito.
Abdulaziz ya kuma bukaci masu tasiri a kafafen sada zumunta da su riƙa tantance gaskiyar bayanai kafin wallafawa tare da gujewa yaɗa abubuwan da za su iya haddasa rarrabuwar kawuna, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana cewa an horas da sama da masu yaɗa saƙonnin APC 100 a kafafen sada zumunta kan yadda za su inganta isar da manufofi da nasarorin gwamnati. Haka kuma ya ƙaddamar da shirin "Gani Ya Kori ji", wani shiri na duba ayyukan ci gaba a jihohin Arewa domin nuna manyan ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnonin Arewa suka aiwatar, waɗanda a cewarsa ba su samu isasshen haske ba.
Da yake buɗe taron a hukumance, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga sauran gwamnatocin jihohi da su yi koyi da shirin Special Reporters Initiative na Kano. Ya ce shirin ya tura matasa sama da 150 zuwa ma'aikatu, hukumomi da kuma dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin inganta sadarwar gwamnati da wayar da kan jama'a.
Taron ya samu halartar 'yan jarida, masu gabatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin, masu shirya fina-finai, masu ƙirƙirar abubuwan dijital, masana, masu tsara manufofi da ƙwararrun masu sadarwa daga sassan Arewacin Najeriya, inda suka tattauna a kan taken "Gwamnati da 'Yan Ƙasa: Riƙon Amana, Nauyi da Ɗa'ar Aikin Yaɗa Labarai."
Comments
Add a comment