Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin karin kudin rajistar jarabawar West African Senior School Certificate Examination (WASSCE) da ta National Examinations Council (NECO) na shekarar 2027, bayan korafe-korafe da kiraye-kirayen da jama'a suka yi na a sake duba matakin.
A cikin wata sanarwa da Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama'a ta Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ta fitar a ranar Litinin, ma'aikatar ta ce ta janye wasikar ranar 18 ga Yunin 2026 da ta sanar da shirin karin kudin domin ba da damar gudanar da tattaunawa mai zurfi da duk masu ruwa da tsaki kafin a yanke hukunci na karshe.
Matakin ya biyo bayan suka da shirin karin kudin ya janyo daga dalibai, iyaye, masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da kungiyoyin farar hula. Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) ma sun yi watsi da shirin tare da bukatar gwamnati ta soke shi saboda tsadar ilimi da ke kara hauhawa.
Ma'aikatar ta ce dakatar da shirin ya biyo bayan umarnin Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, wanda ya bukaci a dakatar da shi domin tabbatar da cewa duk wata manufa ta gwamnati ta kasance bisa gaskiya, hadin gwiwa da kuma hujjoji.
Ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bayan la'akari da damuwar da 'yan Najeriya suka nuna, tare da jaddada cewa karin kudin ya samo asali ne daga tashin kudin gudanar da jarabawar kasa, ciki har da sufuri, tsaro, buga takardun jarabawa, amfani da fasaha da tabbatar da inganci.
Ma'aikatar ta kara da cewa za a gudanar da sabuwar tattaunawa da hukumomin shirya jarabawa, ma'aikatun ilimi na jihohi, masu makarantu, iyaye, kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa duk wata shawara da za a yanke nan gaba za ta kasance mai adalci, gaskiya, dorewar kudi da kuma la'akari da halin tattalin arzikin kasa ba tare da hana dalibai damar samun ilimi ba.
Ta kuma tabbatar da cewa shirin karin kudin ba zai fara aiki ba har sai an kammala wannan tattaunawa, tana mai jaddada cewa jin dadin dalibai da samar da ilimi mai inganci na ci gaba da kasancewa cikin manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu a bangaren ilimi.
Comments
Add a comment